Isa ga babban shafi
Faransa-Zanga-Zanga

Jami'an tsaron Faransa sun kame masu zanga-zanga 700

Ministan harkokin cikin gida na Faransa Laurent Nunez ya ce yanzu haka hukumomi a kasar sun kame mutane 700 masu tayar da hankali a cikin zanga-zangar adawa da shirin karin farashin man fetur na gwamnatin kasar cikin fiye da mutane dubu 31 da suka fito zanga-zangar a yau Asabar.

Mako uku kenan a jere ana gudanar da kazamar zanga-zangar a biranen Faransa wadda kawo yanzu ta juye zuwa rikici duk da matakin gwamnati na dakatar da shirin karin farashin man da dangoginsa.
Mako uku kenan a jere ana gudanar da kazamar zanga-zangar a biranen Faransa wadda kawo yanzu ta juye zuwa rikici duk da matakin gwamnati na dakatar da shirin karin farashin man da dangoginsa. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

A jawaban da ya gabatar bayan tsanantar zanga-zangar yau Asabar da ta kai ga kone-kone yayinda ‘yan sanda ke ci gaba da amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar, ya ce a iya birnin Paris mutane dubu 8 ne suka amsa kiran zanga-zangar nuna kyamar ga manufofin gwamnatin shugaba Emmanuel Macron.

Mako uku kenan a jere ana gudanar da kazamar zanga-zangar a biranen Faransa wadda kawo yanzu ta juye zuwa rikici duk da matakin gwamnati na dakatar da shirin karin farashin man da dangoginsa.

Tuni dai wasu shugabannin kasashe ke ci gaba da jan kunnen al'ummarsu game da ziyarar kasar ta Faransa a halin da ake ciki na zazzafar zanga-zanga.

A bangare guda, zanga-zangar ta haddasa tarin koma baya ga tattalin arzikin kasar duk kuwa da matakin neman sasantawa da shugabannin masu zanga-zangar baya ga daukar matakin dakatar da shirin karin farashin na man fetur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.