Isa ga babban shafi
Faransa

Macron zai gabatar da jawabin farko bayan soma zanga-zanga

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai gana da shugabannin kungiyoyi da ‘yan kasuwa, daga bisani kuma zai yiwa al’umma jawabi kan nemo hanyar warware zanga-zangar dake neman durkusar da kasar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Reuters
Talla

Fadar shugaban kasa tace shugaba Emmanuel Macron zai yi jawabin ne da misalin karfe 8 na daren yau, wanda zai zama jawabin sa na farko bayan kwashe makonni 4 ana gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a fadin kasar.

Jami’an gwamnatin sa sun ce yayin jawabin, shugaban zai gabatar da wasu sabbin shirye shirye domin shawo kan bukatun da masu zanga-zangar suka gabatar.

Ana ta samun kiraye kiraye daga sassan kasar wajen ganin shugaba Macron ya dauki mataki mai kwari domin magance matsalolin da jama’a ke fuskanta, cikin masu kiran harda shugabar Yan ra’ayin rikau Marine Le Pen.

Kakakin gwamnati Benjamin Griveaux, yace sun fahimci bukatun jama’a kuma zasu mayar da martani, yayinda ministan kudi Bruno Le Maire ya koka bisa yadda makwannin da aka kwashe ana zanga-zangar sun haifar da matsalar tattalin arziki wajen lalata hanyoyi da kuma rufe shagunan ‘yan kasuwa da katse yawon bude ido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.