Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

Theresa May ta nuna gamsuwa a ganawarta da shugabannin EU

Firaministar Birtaniya Theresa May ta ce nan da kwanaki kadan za ta koma Brussels don sake tattaunawa da shugabannin Tarayyar Turai wanda kuma a lokacin ne ta ke fatan kammala sauye-sauyen da Majalisar kasar ke neman a gudanar a yarjejeniyar ficewarta daga EU.

A taron da aka shafe kwanaki 2 ana yi a Brussels bayan kadawa Theresa May kuri'ar yankan kaunar da ta sha da kyar a majalisar kasar, taron ya amince da sake wani zama don tattauna bukatar ta May.
A taron da aka shafe kwanaki 2 ana yi a Brussels bayan kadawa Theresa May kuri'ar yankan kaunar da ta sha da kyar a majalisar kasar, taron ya amince da sake wani zama don tattauna bukatar ta May. REUTERS/Piroschka van de Wouw
Talla

A jawabanta ga manema labarai dai dai lokacin da ake karkare taron EU na kwanaki biyu da ke gudana a Brussels wanda EU ta kira bayan Majalisar Birtaniya ta shirya kadawa Firaministar kuri’ar yankan kauna, Theresa May ta ce ilahirin shugabannin kungiyar sun nuna amincewarsu da tattaunawar nan gaba kadan don samar da mafita ga shugabar wadda ke fuskantar matsin lamba kan shirin a cikin gida.

Sai dai Ilahirin shugabannin kasashen na EU 27 sun nuna shakku ga yiwuwar sauya yarjejeniyar shirin ficewar Birtaniyar wadda aka shafe kusan shekaru 2 ana tattauna akan ta, adai dai lokacin da ya rage ‘yan watanni kasar ta kammala ficewa daga EU.

EU dai na ganin yarjejeniyar da ta cimma da Birtaniya ita ce mafi dacewa da kuma nuna halasci da ta yiwa kasar, inda a bangare guda Majalisar Birtaniyar ta yi watsi da ita tare da neman kada kuri’a kan ta a makon jiya kafin daga bisani ta dage zuwa watan Janairun sabuwar shekara.

Majalisar dai na ganin yarjejeniyar da May ta cimma da EU ta bar baya da kura musamman ga wasu muhimman bukatun kasar.

Kowanne lokaci daga mako mai kamawa Theresa May za ta dawo Brussels don ci gaba da tattaunawar da EU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.