Faransa
Yan Sanda sun kashe dan bindigar Strasbourg
‘Yan sanda a Faransa sun kashe Cherif Chekatt, dan bindigar da ya kashe mutaune uku tare da raunata wasu 13 a birnin Strasbourg da ke gabashin kasar, bayan da aka share tsawon kwanaki biyu ana farautar sa.
Wallafawa ranar:
Talla
Chekatt mai shekaru 29 a duniya, an baza jami’an tsaro sama da 700 domin killace unguwar da ya boye bayan kai wannan hari, kuma ministan cikin gidan Faransa Christophe Castaner, ya yi karin bayani a game da yanayin da aka hallaka dan bindigar.
Yan Sanda sun hallaka Cherif Chekatt
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu