Dubban Jama'a sun tsunduma zanga-zangar kyamar Gwamnati a Hungary
An cigaba da gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin Firaminista Viktor Orban na kasar Hungary, inda dimbin masu tarzoma su ka mamaye ginin tashar talabajin na kasar da su ke zargi da mara wa firaministan baya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tarzoma ta barke ne bayan da firaministan ya yi nasarar samun goyon bayan ‘yan majalisa wajen amincewa da sabuwar dokar ayyukan kwadago a kasar, dokar da mafi yawan jama’a ke bayyanawa a matsayin bautar da jama’a.
A wata Afrilun shekarar 2018 ne Jam’iyyar Firaminista Viktor Orban ta yi nasarar lashe zaben ‘yan Majalisar dokoki da aka gudanar a kasar Hungary, abin da zai ba shi damar ci gaba da rike mukaminsa karo na uku a jere.
Mr. Orban na matukar adawa da kara wa Kungiyar Tarayyar Turai karfi a nahiyar, yayin da ya gina yakin neman zabensa akan tubalin kiyayya da karbar baki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu