Isa ga babban shafi
Birtaniya-Kirsimeti

Sarauniyar Ingila ta bukaci kawo karshen nuna wariyar jinsi

Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta biyu ta yi gargadi kan yadda dabi'ar nuna wariyar jinsi ko fifita kabila ko kuma addini ke ci gaba da zama ruwan dare tsakanin al'umma, matakin da ta bayyana da ginshikin haddasa rarrabuwar kan jama'a. 

A cewar Sarauniya Elizabeth babu al'ummar da za ta ci gaba matukar ta dauki dabi'ar nuna wariya.
A cewar Sarauniya Elizabeth babu al'ummar da za ta ci gaba matukar ta dauki dabi'ar nuna wariya. REUTERS/Hannah McKay
Talla

Sarauniya Elizabeth mai shekaru 92 cikin sakon Kirsimetin da ta gabatar ga jama'a na mintuna 5 ta ce rike al'adu na ta ka muhimmiyar rawa wajen gina al'umma amma kuma a bangare guda kan al'umma na rabewa sanadiyyar nuna wariyar jinsi da kabilu ko Addini.

Kalaman na Sarauniya na zuwa bayan makamancinsa daga bakin shugaban darikar Katalika ta duniya Fafaroma Francis da ke neman kawo karshen rarrabuwar kai tare da rungumar zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.