Isa ga babban shafi
Isara'ila-Faransa

Isra'ila na fuskantar babbar barazana daga kasashen Duniya

Kasashe da dama ne a Duniya suka nuna damuwa dama adawar su dangane da matakin Isra’ila na ci gaba da gine-gine a yankunan Falesdinawa.Faransa daga cikin kasashen ta bukaci Isra’ila da ta soke shirin samar da gidaje kusan 2000 a yankin zirin gaza .

Gidajen da Isra'ila ta gina a yankin Falesdinawa
Gidajen da Isra'ila ta gina a yankin Falesdinawa
Talla

Gwamnatin Faransa a jiya alhamis ta bukaci gwamnatin Isra’ila da ta sake duba matakin da ta dau na cigaba da gine-ginen gidaje 2.200 a wasu yankunan Falesdinawa da kasashen Duniya suka nuna adawa a kai.

Hukumar dake tafiyar da sa idanu a ayukan da suka shafi tafiyar da rayuwar farraren fula a kasar ta Is’ra’ila da kuma ke sa ido zuwa ga ayukan da suka shafi gine –gine a ranar litinin da ta gabata ta bayar da nata goyan wajen gina gidaje 2191, matakin da Faransa ta fito filin tareda bayyana adawar ta a kai.

Mai Magana da sunan yahun Ministan harakokin wajen Faransa Agnes Von Der Muhll ta yi kira zuwa hukumomin Isara’ila da su dakatar da wannan aiki ,wanda ke ban hannun da dokokin kasa da kasa da kuma ya sabawa kudurorin majalisar Dinikin Duniya ga baki daya.

A cewar jami’ar diflomasiyar Faransa a ayar doka mai lamba 2334 na kwamitin tsaron majalisar dinkin Duniya, cigaba da mamaye filayen Falesdinawa tareda cigaba da gina gidaje ya sabawa matakin Majalisar Dinkin Duniya da ya shafin dokokin kare bil Adam da na kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.