Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya yi barazanar rufe iyakokin Amurka da Mexico

Shugaban Amurka Donald Trump, yayi barazanar rufe baki dayan iyakokin kasar da Mexico, muddin ‘yan majalisu suka ki amincewa da bukatarsa ta neman dala biliyan 5 domin gina ganuwa tsakaninsu da kasar ta Mexico.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Sabuwar barazanar ta Shugaba Trump, tamkar karin fami ne, kan takaddamar dake tsakaninsa da ‘yan majalisu dangane da batun na gina ganuwa, lamarin da ya haddasa dakatar da wasu muhimman ayyukan akalla 9 daga cikin 15 na ma’aikatun tarayyar kasar.

Mai’aikatun da takaddamar ta shafa sun hada da ma’aikatar tsaron cikin gida, sufuri, ma’aikatar ayyukan gona da kuma ta shari’a.

Hakan yasa tilas dubban wadanda ke aiki a ma’aikatun za su ci gaba da aiki ba tare da albashi ba, ko kuma su tafi hutun tilas na wucin gadi shi ma babu karbar albashin, lamarin da ya shafi ma’aikatan tarayya akalla dubu 800.

‘Yan Democrats da wasu ‘yan majalisun kasar na jam’iyyar Republican na kallon bukatar ta gina ganuwar a matsayin almubazzaranci kuma matakin da bai zama dole ba, yayin da da dama daga cikinsu na jam'iyyar ta Republican mai mulki ke marawa bukatar ta Trump baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.