Kakakin gwamnatin Faransa ya ketare rijiya da baya
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sake bayyana damuwar a wani sako da ya tura ta Twitter, biyo bayan zanga-zangar kungiyoyin nan sanye da riguna masu kalar dorowa da suka sake gudanar da zanga-zanga mako na takwas a sassan kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaba Macron ya bayyana cewa bai dace wasu mutane da sunan masu zanga-zanga su ci gaba da ruguza kokarin hukumomin kasar bayan da gwamnati ta sanar da cewa za ta shafe wasu daga cikin hawayen masu zanga-zanga.
An dai bayyana cewa akalla masu zanga-zanga dubu 50 ne suka sake fitowa a jiya .
Yan Sanda sun yi nasara kubutar da kakakin gwamnatin kasar Faransa Benjamin Griveaux bayan da wasu masu boren suka kutsa cikin ofishin sa dake a yan mituna da ofishin Firaministan kasar Edouard Phillipe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu