rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dubban masu zanga-zanga sun sake fita a Faransa

media
Wasu daga cikin dubban masu rigunan dorawa a birnin Paris na Faransa da ke zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Emmanuel Macron. AFP/Geoffroy van der Hasselt

Dubban masu zanga-zanga sun yi tattaki a biranen kasar Faransa yau Asabar, bayan amsa kiran masu sanye da rigunan dorawa da suke jagorantar zanga-zangar adawa da shugabancin Emmanuel Macron.


Sabunta zanga-zangar ya zo ne bayan shan alwashin da hukumomin Faransa suka yi na hukunta masu tada rikici yayin zanga-zangar, hakan tasa aka aike da jami’an tsaro dubu 80, zuwa sassan kasar domin dakile duk wani yunkuri na tayar da tarzoma.

A Paris kadai ‘yan sanda dubu 5, aka girke, la’akari da cewa a birnin aka fi samun tarzoma gami da arrandama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaron.

Ma’aikatar cikin gidan kasar ta ce akwai yiwuwar yawan wadanda suka yi zanga-zangar ta yau, ya zarta mutane dubu 50, da suka fita a makon da ya gabata.

A makon da ya gabata ne dai Firaministan Faransa, Edouard Philippe ya bayyana shirin gwamnatin kasar na haramta zanga-zangar da ta saba ka’ida, yayin da mahukuntan kasar ke ci gaba da fafutukar kawo karshen zanga-zangar masu sanye da riguna launin dorawa.

Wannan na zuwa ne bayan wasu kusoshi biyu na jam’iyya mai mulkin Italiya sun bayyana goyon baya ga masu zanga-zangar , suna masu zargin gwamnatin Faransa da nuna halin-ko-in-kula ga talakawan kasar.