Isa ga babban shafi
Amurka

Gurguncewar ma’aikatun Amurka ya zama mafi tsawo a Tarihi

Gurguncewar da ayyukan wasu muhimman ma’aikatun gwamnatin Amurka su ka yi na wucin gadi a baya bayan nan, ya zama mafi tsawo da aka taba gani a Tarihin kasar.

Daya daga cikin masu zanga-zanga kan dakatar da ayyukan wasu muhimman ma'aikatun kasar Amurka.
Daya daga cikin masu zanga-zanga kan dakatar da ayyukan wasu muhimman ma'aikatun kasar Amurka. Carlos Barria/Reuters
Talla

A halin yanzu dai dakatar da ayyukan ma’aikatun gwamnatin na Amurka ya shiga rana ta 22, lamarin da ya shafi sama da ma’aikata dubu 800 a matakin tarayya.

Lamarin dai ya samo asali daga takaddama tsakanin shugaban Amurkan Donald Trump da ‘Yan Majalisu, bayan da suka ki amincewa da bukatarsa ta neman dala biliyan 5 domin gina katafariyar katanga tsakanin Amurkan da Mexico.

Rabon da ga irin wannan mataki na dakatar da ayyukan muhimmai daga ma’aikatun Amurka, a dalilin sabanin Majalisar da bangaren zartaswa, tun a shekarar 1995 zuwa 1996, a zamanin mulkin Bill Clinton, lokacin da ma’aikatun suka shafe kwanaki 21 suna cikin yanayi na dakatar da ayyukansu na wucin gadi.

Da fari dai shugaba Trump yayi barazanar yin amfani da karfin dokar ta baci da kundin tsarin mulki ya bashi dama, wajen yin amfani da kudin, amma ya janye kudurin nasa daga bisani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.