Isa ga babban shafi
Birtaniya-EU

EU ba za ta sauya yarjejeniyar da muka cimma kan ficewa ba - May

Firaministar Birtaniya Theresa May ta gargadi Majalisar kasar kan yunkurin sake kada kuri’a ga yarjejeniyar da ta cimma da EU, ta na mai cewa Tarayya Turai ba za ta amince da kulla wata sabuwar yarjejeniya da kasar ba.Kalaman May na zuwa sa’o’I kalilan bayan wasikar da kungiyar ta EU ta aike mata kan cewa bazata amince da sake wata yarjejeniya da kasar kan shirin ficewar ba.

A gobe ne dai Majalisar Birtaniyar za ta yi zama kan batun wanda ake sa ran ta karkare matakin da ya kamata ta dauka game da yarjejeniyar ficewar kasar daga EU.
A gobe ne dai Majalisar Birtaniyar za ta yi zama kan batun wanda ake sa ran ta karkare matakin da ya kamata ta dauka game da yarjejeniyar ficewar kasar daga EU. Ben Birchall/Pool via REUTERS
Talla

Cikin jawaban da Theresa May ta gabatar ta ce kungiyar tarayyar Turai ta bata tabbacin ba za ta amince da duk wani yunkurin samar da sauyi ga yarjejeniyar da ta cimma da ita ba, dai dai lokacin da ya rage kasa da watanni 2 kasar ta kamala ficewa daga EU a hukumance, inda ta ce hakan na nuna cewa kada kuri’ar kalubalantar yarjejeniyar zai mayar da kasar baya daga nasarar da ta riga ta cimma a shirin na ta na ficewa.

Tun da safiyar yau litinin ne, Birtaniyar ta wayi gari da jerin wasikun shugaban kungiyar tarayyar Turai Jean-Claude Junker da shugaban Majalisar kungiyar Donald Tusk wadanda a ciki su ke tabbatarwa kasar cewa baza su sake wani sabon zama game da yarjejeniyar da ta tabo batun makomar yankin Ireland.

Cikin jawaban na May wanda ta gabatar a tsakiyar birnin Stoke na yankin Ingila, yankin da ke mara baya ga shirin ficewar, ta ce yanzu kam ta tabbata dole majalisar ta karbi yarjejeniyar ta kuma yi aiki da ita, duba da cewa babu wani gurbin sauya ta a can Majalisar Turai.

A gobe Talata Majalisar za ta yi zama na musamman kan batun yayinda May ke da tarin masu kalubalantarta ciki har da ‘yan Jam’iyyarta da kuma ilahirin ‘yan majalisun yankin Ireland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.