Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

Majalisar Birtaniya ta yi watsi da yarjejeniyar ficewar kasar daga EU

Majalisar Birtaniya ta kada kuri'ar kin amincewa da yarjejeniyar da Firaminista Theresa May ta cimma da kungiyar EU karkashin shirin gwamnatin kasar na ficewa daga kungiyar tarayyar Turai.

Ko a watan Disamban da ya gabata ma. May ta fuskanci makamanciyar kuri'ar yankan kaunar daga mambobin Majalisar na Jam'iyyarta amma ta sha da kyar.
Ko a watan Disamban da ya gabata ma. May ta fuskanci makamanciyar kuri'ar yankan kaunar daga mambobin Majalisar na Jam'iyyarta amma ta sha da kyar. Reuters
Talla

A zaman kada kuri'a kan yarjejeniyar da Theresa May ta cimma da EU wanda ya gudana a yau Talata, 'yan majalisu 432 ne suka yi watsi da yarjejeniyar yayinda wasu 202 suka goyi bayanta.

Tuni dai shugaban marasa rinjaye na Majalisar Jeremy Corbyn ya gabatar da bukatar kada kuri'ar yankar kauna ga Theresa May wanda ya bukaci a tafka muhawara kan batun a gobe Laraba.

Ko a watan Disamban da ya gabata ma. May ta fuskanci makamanciyar kuri'ar yankan kaunar daga mambobin Majalisar na Jam'iyyarta amma ta sha da kyar.

Yanzu haka dai ya ragewa May ko dai ta janye batun ficewar dungurugum ko kuma kasar ta fice ba tare da cimma yarjejeniya da EU ba ko kuma ta koma cikin gungun kasashen kungiyar ta EU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.