rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Venezuela Amurka Donald Trump Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Maduro ya bai wa jami’an Amurka sa’o’i 72 su fice daga Venezuela

media
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro. REUTERS/Manaure Quintero

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, ya bai wa jami’an diflomasiyyar Amurka sa’o’i 72 su fice daga kasar, biyo bayan matakin shugaba Donald Trump na goyon bayan kawar da gwamnatinsa.


Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce shugaba Maduro ba shi da wani iko a hannunsa da zai iya daukar wannan mataki.

A ranar Laraba 23 ga watan Janairu, jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, kuma shugaban majalisar dokokin kasar, ya nada kansa a matsayin sabon shugaba, bayan shafe tsawon lokaci yana bayyana gwamnatin Maduro a matsayin haramtacciya.

Jim kadan bayan sanarwar Guaido, shugaban Amurka Donald Trump ya aike da sakon goyon bayansa, inda ya sha alwashin yin amfani da dukkan karfin Amurka na Tattalin Arziki da Diflomasiyya, wajen kawar da gwamnatin shugaban kasar ta Venezuela mai ci Nicolas Maduro, wadda ya bayyana a matsayin haramtaciyya, la’akari da zabe mai cike da magudi da ya kafa ta a watan Mayu na shekarar bara.

A halin yanzu dai dubban ‘yan kasar ta Venezuela na ci gaba da yin zanga-zanga a biranin kasar, kuma alkalumma na nuni da cewa mutane 13 ne suka rasa rayukansu, mafi akasari kuma an harbe su ne da bindiga.

Sai dai fa zanga-zangar da ke gudana a Venezuelan ta zo ne ta fuskoki biyu, domin yayin da dubban ‘yan kasar ke zanga-zangar adawa da gwamnatin Maduro, wasu dubban kuwa na gudanar da tasu ce don nuna goyon bayansu ga shugaban, a dai dai lokacin da kasar ke bikin tunawa da ranar juyin juya halinta.