rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tattalin arzikin Faransa ya fuskanci koma baya a 2018

media
Sai dai duk da hasashen na wannan cibiya har yanzu tattalin arzikin Faransar na nan da karfinta a cewa ministan tattalin arzikin kasar Bruno Le Maire. REUTERS/Emmanuel Foudrot

Tattalin arzikin Faransa ya fuskanci koma baya a shekarar da ta gabata ta 2018 sakamakon girgizar da tattalin arzikin duniya ya yi matakin da ya haifar da matsin rayuwa ga al’umma abin da ake ganin ya assasa zanga-zangar masu yaluwar riga a kasar.


Hasashen farko da cibiyar hasashen tattalin ariziki ta INSEE ta wallafa a yau laraba, ya nuna cewa a shekarar da ta gabata kashi 1.5% ne kawai suka shiga aljihun gwamnati daga kudaden da ta yi hasashen samu a cikin gida, wanda ya kasa nesa ba kusa ba idan aka auna da shekara ta 2017.

Sai dai kuma sakamakon na kashi 1.5% da aka samu a shekarar da ta gabata ta 2018 ya yi kasa kan burin da gwamnati ta yi hasashen samu na kashi 1.7% bayan da ta yi fatan samun ci gaba da akalla kashi 2.

A rubu'in na 4 na shekarar da ta gabata lamuran tattalin arziki a Faransa sun ja baya fiye da yadda aka yi tsammani, inda ta samu kasa da kashi daya dai dai da 0.3% na kudaden shigar da aka samu, sakamakon da ya kasa wajen cike gibin shekarar da ta gabata.

Haka zalika za a iya cewa duk da lalacewar yanayin tattalin arzikin duniya, da kuma zanga-zangar masu yaluwar riga, tattalin arzikin Faransa na da karfinsa, kuma siyasar tattalin arzikin da gwamnati ta dauka ya haifar da da mai ido a cewar ministan tattalin arzikin kasar Bruno Le Maire.