Isa ga babban shafi
Venezuela

Guaido zai nemi goyon bayan sojojin Venezuela don kawar da Maduro

Mutumin da ya bayyana kan sa a matsayin shugaban riko na Venezuela Juan Guaido, ya ce samun goyan bayan sojojin kasar na da matukar tasiri wajen kawar da shugaba Nicolas Maduro daga mulki.

Jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa.
Jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa. REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

Guaido ya ce yayi taro a asirce da wasu daga cikin sojojin inda suka bayyana masa cewar ba zasu bari a cigaba da tafiyar da kasar kamar yadda ake yanzu ba.

Guaido ya shaidawa Jaridar New York Times cewar janye goyan bayan sojin da Maduro ke da shi ya zama dole kafin sauya gwamnati.

Shugaba Donald Trump yace ya tattauna da Guaido ta waya inda ya sake jaddada masa goyan bayan Amurka.

A makon da ya gabata, jagoran ‘yan adawar na Venezuela kuma shugaban majalisar dokokin kasar Juan Guaido, yayi watsi da tayin tattaunawar sulhu tsakaninsa da shugaba Maduro, a dai dai lokacin da wasu kasashen duniya ke kira ga Maduro ya soke zaben watan Mayu na bara, da ya bashi damar shugabanci wa’adi na 2, ya kuma shirya sabon zabe nan da ‘yan kwanaki, wanda zai karbu ga kowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.