rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Nukiliya Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rasha ta sha alwashin kera sabbin makamai masu linzami

media
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Fuente: Reuters.

Rasha ta sha alwashin kera sabbin muggan makamai, iri daban daban, bayan da a jiya Asabar ta dakatar da yarjejeniyar haramta kera makamai masu linzami da takaita yaduwarsu da ke tsakaninta da Amurka.


Matakin na Rasha, martani ne kan yadda a juma’ar da ta gabata, Amurka ta bayyana soma aiwatar da shirin ficewa daga yarjejeniyar ta shekarar 1987, bayan da ta zargi Rasha da sabawa ka’aidojin haramta kera makamai masu linzami da ke cin matsakaicin zango, dake tafiyar nisan kilomita 500 zuwa dubu 5000.

Muddin aka gaza warware takaddamar da ta kunno kai tsakanin Amurkan da Rasha, akwai fargabar cewa kasashen biyu za su kulla gasar kera muggan makamai, abinda suka cimma matsayar dakatarwa sama da shekaru 30 da suka gabata.

A shekarar 1987 shugaban Amurka Ronald Regan da takwaransa na tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev suka rattaba hannu kan yarjejeniyar haramta kera nau'ikan makamai masu linzami, wadanda ke iya shafe nisan kilomita 500 zuwa dubu 5, zalika cikin matukar sauri da baya wuce mintuna suke isa wurin da suka nufa.