Isa ga babban shafi
Himalaya

Kankarar tsaunukan Himalaya ka iya narkewa nan da wasu shekaru

Wani binciken masana ya nuna cewar kashi biyu bisa uku na Yankin duniya da ake kira tsaunukan Himalaya da ke fama da tsananin sanyi na iya narkewa nan da shekarar 2100 muddin ba’a magance matsalar sauyin yanayin da ake samu ba.

Yankin dai na samar da ruwa ga akalla manyan tekunan duniya 10
Yankin dai na samar da ruwa ga akalla manyan tekunan duniya 10 Reuters
Talla

Masanan kimiyan sun ce, ko da an aiwatar da yarjejeniyar Paris ta rage dumamar yanayin da ake samu na maki daya da rabi, kashi daya bisa uku na Yankin Himalaya zai narke.

Rahotan binciken ya ce Yankin na samarwa akalla mutane sama da miliyan 250 ruwan sha da kuma wasu sama da biliyan daya da rabi da ke amfana da ruwan da su ke samu a tafkuna.

Masanan sun ce wasu manyan tafkuna 10 da ake da su a duniya duk suna samun ruwan su ne daga wannan yankin cikin su har da Ganges da Indus da Yellow da Mekong da Irrawaddy.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.