rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Malisar dokokin Faransa ta amincewa yan sanda su yi amfani da karfi

media
shugaban Faransawa Emmanuel Macron a taron magadiyan gari 15 janairu 2019. REUTERS/Philippe Wojazer/Pool

Majalisar dokokin Faransa ta kada kuri’ar amincewa da wani kudirin doka da ke baiwa jami’an tsaro damar dakile zanga-zanga tare da hukunta masu aikata tarzoma, a wani kokarin gwamnatin kasar na kawo karshen tarzomar masu sanye da riguna mai launin dorowa.


A Karkashin wannan dokar dai jami’an gwamnati ka iya hana duk wani da ake ganin dan jagaliya ne shiga zanga-zanga ba sai anbi ta kotu ba.

Dokar dai ta samu amincewar ‘yan majalisu 387, yayin da 87 sukaki amincewa, wanda ‘yan adawa ke cewa ta yi hannun riga da ‘yancin ‘yan kasar na gudanar da zanga-zanga.

Cikin ‘yan majalisun da sukaki amincewa da dokar harda wasu 50 daga jam’iyyar shugaban kasar Emmanuel Macron, abinda ke tattabatar da rarrabuwar kawuna kan batun.

Idan har majalisar dattawa suka aminta da kuma kutun tsarin mulki, za’a hukunta duk wanda aka kama da laifi daurin watanni shida da kuma taran Euro 7, 500.

Haka zalika dokar tayi tanadin daurin shekara daya da kuma taran Euro 15000, ga wadanda ke rufe fuskokinsu don bat da kama yayin gudanar da zanga-zanga.