rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Emmanuel Macron Italiya Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta janye jakadanta daga Italiya

media
Mataimakin Fira Ministan Italiya, Luigi Di Maio. AFP/Alberto Pizzoli

Gwamnatin Kasar Faransa tace ta kira Jakadanta dake Italiya domin ganawa da shi sakamakon takalar da take ci gaba da fuskanta daga gwamnatin Italiya.


Wannan ya biyo bayan ganawar da akayi tsakanin kungiyar masu adawa da shugaba Emmanuel Macron da mataimakin Fira ministan Italiya Luigi Di Maio.

Gwamnatin Faransa ta hannun ma’aikatar harkokin wajenta tace daukar matakin kiran Jakadanta gida ya biyo bayan watannin da aka kwashe ana takun saka da Italiya wadda ke zarge-zarge marasa tushe da makama, wanda take cewa shi ne irin san a farko tun bayan yakin duniya na biyu.

Takaddama tsakanin kasashen biyu yayi kamari ne tun a watan Yunin bara, lokacin da gwamnatin yan ra’ayin rikau ta karbi ragamar tafiyar da kasar ta Italiya.

Manyan jami’an gwamnatin kawancen kasar sun kawar da kimar diflomasiya wajen sukar shugaba Emmanuel Macron wanda ya fito karara yake yaki da manufofi irin nasu.

Rikicin yayi zafi ne ranar Talatar da ta gabata, inda mataimakin Fira ministan Italiya Luigi Di Maio yace ya gana da shugabannin masu zanga-zangar adawa da shugaba Macron a wajen birnin Paris domin hada kai da su wajen kada Macron a zaben Yan Majalisun Turai mai zuwa.

Shima kan sa Fira minista Matteo Salvini baya ragawa shugaba Macron wajen cacakar manufofin sa gaba da gaba, inda ya bukaci Faransawa da su kawar da shi daga karagar mulki.