rfi

Saurare
 • Labarai Kai-tsaye
 • Labaran da suka gabata
 • RFI duniya
 • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
 • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia
 • Yau ake zama a bainin jama'a game da tsige Shugaban Amurka Trump
 • Wasu 'yan kasar Kamaru sun shiga Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.
 • Tashin Bam a Kabul na Afghanistan ya kashe mutane 7
 • Saudiya, Daular Larabawa da Bahrain za su shiga wasannin kwallon kafa tare
 • Hari daga Israila ya kashe Bafalastine daya
 • Amurka ta gargadi 'yan kasar daga zuwa Bolivia

ISIL Ta'addanci Jamus Angela Merkel Syria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Har yanzu kungiyar ISIS babbar barazana ce ga tsaro - Merkel

media
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel. REUTERS/Costas Baltas

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta yi gargadin cewa, ko kusa dakarun kawancen kasashen duniya ba su yi nasarar murkushe mayakan Kungiyar ISIS ba.


Merkel wadda ta yi gargadin a wannan JumaĆ” a birnin Berlin, ta ce duk da rasa yankunan da mayakan na ISIS suka yi, wadanda a baya suka mamaye musamman a Syria, har yanzu Kungiyar tana tattare da babbar barazana tsaro.

Kalaman na Shugabar gwamnatin, sun ci karo da ikirarin shugaban Amurka Donald Trump, wanda a watan Disambar ya ce dakarunsa sun yi nasarar murkushe mayakan na ISIS a Syria, inda kuma yayi alkawarin janye sojojin Amurka dubu 2 da ke taimakawa mayakan Kurdawan YPG wajen yakar Kungiyar ta ISIS.

A karshen watan Afrilu da ke tafe ake sa ran kamala janyewar sojojin Amurkan dubu 2 da ke Syria, kamar yadda shugaba Trump yayi alkawari.

Sai dai matakin ya jefa kasashen yammacin Turai cikin shakku da fargabar mai yiwuwa, Kungiyar ta ISIS ta sake bayyana da cikakken karfi, bayan janyewar dakarun na Amurka, idan aka gaza cimma nasarar warware yakin basasar kasar ta Syria.