rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Emmanuel Macron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Babban mashawarcin Emmanuel Macron ya yi murabus

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Ismael Emelien mashawarcinsa na musamman da ya yi murabus Reuters

Guda cikin manyan Mashawartan shugaban Faransa Emmanuel Macron Ismael Emelien ya sanar da murabus dinsa a yau, dai dai lokacin da shugaban ke kokarin farfado da farin jininsa bayan boren da ya ke fuskanta daga al’ummar kasar sanadiyyar wasu manufofinsa.


Ismael Emelien matashi mai shekaru 31 na daga cikin jiga-jigan da suka taka muhimmiyar rawa wajen yada manufofin shugaba Emmanuel Macron tun kafin zaben kasar na shekarar 2017, kazalika shi ne mukarraban shugaban na biyu da ke sanar da murabus a baya-bayan nan tun bayan boren da Macron ke fuskanta kan sabbin manufofinsa game da tattalin arziki.

Emelien wanda mawallafin littafi ne, ya kuma rike matsayin babban mashawarcin shugaba Emmanuel Macron tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2017, da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, ya ce ajje mukaminsa ba murabus ba ne inda ya ce ya tafi ne don yin wani rubutu na musamman kan siyasar masu sassaucin ra’ayi.

Tsohon mashawarcin na musamman ga Emmanuel Macron, wanda a baya ke kauracewa tattaunawa da manema labarai, ya ce duk wata fassara da za a yiwa tafiyarsa, hakan baya nufin ya juya baya ga gwamnati face samun damar gudanar da nazari.

Matashin mashawarcin ana ganin na daga cikin masu bayar da shawara ta bayan fage ga Emmanuel Macron kan yadda zai gabatar da jawaban siyasa ko kuma mayar da martini ga bangarorin adawa.