Isa ga babban shafi
SPAIN

Firaministan Spain ya bukaci zaben gaggawa

Firaministan Spain, Pedro Sanhez ya bukaci gudanar da zaben gaggawa nan da watan Aprilu mai zuwa, bayan Majalisar Dokokin Kasar ta yi watsi da kudirin kasafin kudin da ya gabatar mata sakamakon rikicin ballewar yankin Catalonia.

Firaministan Spain, Pedro Sanchez
Firaministan Spain, Pedro Sanchez REUTERS/Juan Medina
Talla

Firaminista Sanchez ya ce, ya gwammaje ya zabi batun bai wa al’ummar Spain damar bayyana ra’ayoyinsu fiye da ci gaba da kasancewa a mukaminsa ba tare da kasafin kudi ba.

Sanchez ya dare kan karaga ne kimanin watanni takwas da suka gabata bayan ya yi nasarar kawar da gwamnatin masu tsattsauran ra’ayi a wata kuri’ar yankar- kauna da aka kada a Majalisar Dokoki. Sai dai tun daga wannan lokacin yake ta fama da wasu matsaloli da suka hada da batun ballewar yankin Catalonia.

A ranar Larabar da ta gabata ne, ‘Yan Majalisar yankin Catalonia suka hada kai da sauran mambobin majalisar masu tsattsauran ra’ayi wajen watsi da kasafin kudin da Mr. Sanchez ya gabatar.

‘Yan Majalisun sun kuma janye daga mara masa baya domin nuna adawarsu ga shugabannin ‘yan aware da ake tuhumar su kan rawar da suka taka a fafutukar ballewar yankin Catalonia daga Spain a shekarar 2017.

Sai dai Firaminstan ya caccaki matakin watsi da kasafin kudin wanda ya kunshi matakan samar wa al’umma kayayyakin more rayuwa bayan kasar ta yi fama da tsuke bakin aljihu na tsawon shekaru, yayin da yake cewa, ta hanyar tattaunawa ne kawai za a iya magance rikicin ballewar Catalonia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.