Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

''Masu ra'ayin rikau za su samu rinjaye a Turai''

Wata Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a ta nuna cewa, masu tsattsauran ra’ayi, ka iya samun nasara a zaben ‘Yan Majalisun Kasashen Turai da za a gudanar a cikin watan Mayu mai zuwa.

Sama da mutane miliyan 300 za su kada kuri'a a zaben 'Yan Majalisun Kasashen Turai
Sama da mutane miliyan 300 za su kada kuri'a a zaben 'Yan Majalisun Kasashen Turai REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Kuri’ar ta nuna cewa, jam’iyyun da ke biyayya ga Ministan Cikin Gidan Italiya mai ra’ayin rikau, Matteo Slavini da kuma Marine Le Pen ta Faransa za su samu nasara.

Sai dai Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’ar ta nuna cewa, tsoffin jam’iyyun siyasa da aka dade ana damawa da su, za su ci gaba da samun rinjaye bayan gudanar da zaben na ‘yan Majalisu, amma akwai alamun da ke nuna cewa, za a samu rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.

Sabbin ‘Yan Majalisu 705 da za a zaba tsakanin ranakun 23-26 ga watan na Mayu, za su taimaka wajen samar da sabbin dokokin Kungiyar Kasashen Turai har nan da shekaru biyar masu zuwa, yayin da za su zabi wanda zai maye gurbin Jean Claude Juncker da ke rike da shugabancin Hukumar Tarayyar Turai.

Zaben na ‘yan Majalisun Turai na daya daga cikin manyan ayyukan demokradiya da ke matukar daukar hankula a duniya, in da kimanin jama’a miliyan 373 daga kasashen Turai 27 za su kada kuri’unsu.

Sai dai mutanen Birtaniya ba za su shiga cikin masu kada kuri ‘ar ba, lura da cewa, kasar za ta kammala ficewa daga gungun kasashen Turai nan da ranar 29 ga watan Maris mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.