Isa ga babban shafi
Spain

Tsohon Firaministan Spain zai gurfana gaban kotu kan 'yan Catalonia

Tsohon Firaministan Spain Mariano Rajoy zai gurfana a gaban kotu ranar 26 ga wannan wata domin bada ba’asi a shari’ar da ake yi wa shugaban Yan awaren Catalonia da suka nemi ballewa daga kasar a shekarar 2017.

Tsohon Firaministan Spain Mariano Rajoy
Tsohon Firaministan Spain Mariano Rajoy REUTERS/Stringer
Talla

Kotun kolin kasar ta sanar da cewar, cikin wadanda ake saran ba da shaida a shari’ar har da tsohon Firaministan da tsohon shugaban Catalonia Artur Mas da kuma tsohon mataimakin Firaminista Soraya Saenz de Santamaria.

Kotun ta ce shima tsohon shugaban Yankin Basque Inigo Urkullu, da ya shiga tsakani lokacin rikicin zai ba da shaida.

A watan Nuwamban 2017 ne yankin na Catalonia karkashin jagorancin Carles Puigdemont ya kada kuri'ar ballewa duk da hanin hakan daga babbar Kotun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.