Isa ga babban shafi
EU-Venezuela

EU ta gargadi kasashe kan yiwa Venezuela katsalandan din Soji

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta gargadi kasashen duniya kan illar yi wa Venezuela katsalandan din Soji a harkokinta, dai dai lokacin da rikici ya dabaibaye kasar da nufin samar da maslahar dimokaradiyya wajen shawon kan rikicin.

Babbar jami'ar kare manufofin diflomasiyyar kasashen Turai a duniya Federica Mogherini
Babbar jami'ar kare manufofin diflomasiyyar kasashen Turai a duniya Federica Mogherini REUTERS/Piroschka van de Wouw/File Photo
Talla

A cewar Maja Kocijancic kakakin shugabar Ofishin kula da manufofin diflomasiyyar Tarayyar Turai a kasashen duniya Federica Mogherini, a wata ganawarta da manema labarai, ta ce babu bukatar sai an sanya karfin soji kafin warware rikicin kasar ta Venezuela, matukar zai iya warwaruwa ta hanyar dimokaradiyya.

Tun a makon da ya gabata ne dai yayin taron shugabannin kasashen Turai da ya gudana a Brussels, suka cimma matsayar kin mara baya wajen amfani da karfin soji a kasar ta Venezuela.

Shima ministan harkokin wajen Spain, Josep Borell, ya shaida wa manema labarai cewa shugabannin Turai sun yi kashedi ga dukannin kasashen da ke tunanin yin katsalandan a Venezuela ta wajen aikewa da dakarunsu cewa ba za su goyi bayan hakan ba, kuma za su soki abin ba kakkautawa.

Jagoran ‘yan adawa a kasar ta Venezuela, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa, Juan Guaido yana birnin Bogota na Colombia inda yake tattaunawa da abokan huldarsa na nahiyar don lalubo hanyar da za a bi wajen tilasta wa shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya sauka daga mukaminsa.

Taron na Bogota na zuwa ne kwanaki biyu bayan mutane biyu sun mutu, daruruwa suka jikkata yayin wata arangama tsakanin magoya bayan Guaido da jami’en tsaron Vnezuela yayin wani kokarin shigowa da kayayyakin agaji daga Colombia da Brazil da ya ci tura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.