Isa ga babban shafi
Belgium-Syria

Kotun Belgium ta yi umarnin kwaso 'yan kasar da ke yaki a Syria

Kotun daukaka kara a Belgium, ta bai wa gwamnatin kasar damar kwaso iyalan mayakan jihadi ‘yan asalin kasar da aka ceto daga hannun mujahidai a fagen da ke Syria, tare da dawowa da su kasar ta Belgium.

Wasu tarin fararen hula kenan wadanda aka tseratar bayan farmakar yankin Deir Ezzor na Syria
Wasu tarin fararen hula kenan wadanda aka tseratar bayan farmakar yankin Deir Ezzor na Syria © RFI / Sami Boukhelifa
Talla

Belguim, Faransa da kuma Birtaniya, na daga cikin kasashen yamma da dama da aka kama ‘yan asalin kasashensu a kasar Syria, bayan da Kurdawa da ke samun goyon bayan dakarun kasashen kawance suka yi wa yankin arewacin kasar kofar rago.

Bayan da aka tabbatar mata cewa akwai yara kanana akalla 6 da aka kwato daga hannun mujahidan, gwamnatin Belgium ta yi kokarin dawo da su gida, to sai dai wata karamar kotun kasar ta bayyana matakin a matsayin wanda ya saba wa ka’ida.

Ita ma dai gwamnatin Syria, ta sanar da cewa masu ikirarin jihadi 350 da kuma fararen hula dubu daya da 400 ne aka kwashe daga yankin Baghouz, wanda ake kallo a matsayin tungar karshe a kasar ta Syria.

Sauran kasashe musamman ma Faransa, yanzu haka na cigaba da nazari dangane da yadda za a dawo mujahidansu da aka cafke a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.