Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta tsaurara haraji kan manyan kamfanonin sadarwa

Gwamnatin Faransa, ta bayyana shirin tilastawa manyan kamfanonin sadarwar Internet na duniya da ke hada-hada a kasar, kara yawan harajin da suke biyanta.

Ministan lura da tattalin arzikin Faransa Bruno Le Maire.
Ministan lura da tattalin arzikin Faransa Bruno Le Maire. AFP/File
Talla

Wasu daga cikin manyan kamfanonin da sabuwar dokar Karin harajin za ta shafa, sun hada da Google, da kuma Facebook.

Sabuwar dokar da gwamnatin Faransa ta gabatarwa majalisar dokokin kasar za ta shafi akalla mayan kamfanonin sadarwar Internet 30 mallakin kasashen Amurka, China, Jamus, Spain, Birtaniya da kuma wadanda ke cikin kasar ta Faransa.

Karkashin dokar, manyan kamfanonin sadarwar da suka kunshi Facebook, Google, Apple da kuma Amazon, za su kara yawan harajin da suke biyan gwamnatin Faransa da kashi 3 cikin dari na ribar hada-hadar kasuwancin da suke yi a kasar, kwatankwacin dala miliyan 566 a jimlace.

A watannin baya shugaban Faransa Emmanuel Macron yayi kokarin ganin an kafa irin wannan doka a nahiyar Turai baki daya karkashin jagorancin kungiyar EU, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

A waccan lokacin kasashen Ireland, Denmark da Sweden ne suka hau kujerar naki, bisa fargabar cewa kamfanonin da dokar za ta shafa, za su janye kasuwancinsu zuwa wasu kasashen na daban, da basu da dokoki masu tsauri kan biyan haraji.

Jamus ma dai ta goyi bayan kin kafa dokar, saboda kaucewa shiga yakin kasuwanci da Amurka, la’akari da cewa gwamnatin Donald Trump ka iya kakabawa motocin da Jamus din ke kaiwa kasuwannin kasar haraji mai tsauri a matsayin martani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.