Isa ga babban shafi
Faransa-Kwastam

Yajin aikin Kwastam a Faransa ya haddasa tsaiko a zirga-zirga

Jami’an Kwastam Faransa sun shiga rana ta hudu da fara yajin aiki, lamarin da ya kawo tsaiko ga harkokin sufuri a kasar musamman a bangaren jiragen kasan Eurostar da ke jigilan fasinjoji tsakanin Paris zuwa London, wanda suka samu tsaikon akalla sa’o’i biyu kan lokutan da suka saba.

Yajin aikin jami'an na Kwastam dai ya haddasa tsaiko a sufurin jiragen kasa, musamman wadanda ke tashi daga birnin Paris su shiga kasar Birtaniya
Yajin aikin jami'an na Kwastam dai ya haddasa tsaiko a sufurin jiragen kasa, musamman wadanda ke tashi daga birnin Paris su shiga kasar Birtaniya REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Tun daga ranar Litinin, jami'an kwastam na manyan tashashon jiragen ruwa na Arewacin Faransa wato tashar Calais da Dunkerque, suka tsunduma yajin aikin don neman ganin an biya musu wasu bukatun su gabanin ficewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar Turai.

Yajin aikin jami'an na Kwastam dai ya haifar da cinkoso da dogon layukan manyan motoci a shingayen bincike, wanda ya haifar da tsaiko ga matafiya Birtaniya da ke makwabtaka da Faransa, ta hanyar karkashin kasa na Manche da kuma tashar ruwar Calais.

A jiya Laraba, ne lamarin ya tsananta bayan da babbar tashar jiragen kasa na Faransa ta Gare du Nord da ke birnin Paris, ta bi suhun masu yajin aiki, baya ga filin jiragen saman kasar na Roissy-Charle de Gaulle da suka mara baya ko da dai shigarsu bai haifar da tsaiko a harkar sufurin jiragen saman kasar ba.

A cewar wani jami’in kamfanin jiragen kasan kasa-da-kasa na Eurostar, lamarin ya shafi ilahirin harkokin sufurin jiragen kasan kasar da ke zuwa Arewacin kasar da tsaikon mintunan 120, sakamokon jinkiri da ake samu a shingayen binciki.

Cikin bukatun Jami’an na kwastam da ke yajin aiki, akwai karin albashi, da kuma karin ma’aikatan gabanin fitcewar Burtaniya daga tarayyar Turai, wanda suke ganin ayyukansu zai karu, sabanin lokacin da Burtaniyar ke Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.