Kotu a Australia ta yanke hukuncin daurin zuwa Cardinal George Pell
Wata Kotu a Australia ta yanke hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari kan wani tsohon babban limamin coci, Cardinal George Pell da aka samu da laifin lalata da wasu yara biyu dake aiki a cocin.
Wallafawa ranar:
Cardinal Pell wanda shine tsohon mutumi na uku a jerin shugabannin mabiya darikar Katolika dake fadar Vatican, wanda ke kula da baitulmali, kana kuma ya taimaka wajen zabo fafaroma guda biyu, ya aikata laifin ne tsakanin shekarar 1996 zuwa 1997.
Alkalin kotun, Peter Kidd ya bayyana halayen Cardinal Pell mai shekaru 77 a matsayin abin takaici da kuma Allah wadai saboda kimar sa da mukamin da ya rike.
Cardinal Pell mai shekaru 77 yace zai daukaka kara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu