Isa ga babban shafi
Faransa-Yanayi

Dubban matasa sun yi zanga-zanga kan sauyin yanayi a Faransa

Dubun dubatar Faransawa galibi matasa sun gudanar da zanga-zangar bukatar daukar matakai kan sauyin yanayi, zanga-zangar da ta gudana bisa matakan tsaro tare da sahalewar hukumomin kasar.

Matasan da suka gudanar da zanga-zangar a sassan kasar ta Faransa
Matasan da suka gudanar da zanga-zangar a sassan kasar ta Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Zanga zangar wadda galibi matasa dalibai suka mamaye ta na da nufin matsawa gwamnati wajen ganin ta dauki matakan da suka kamata wajen yakar sauyin yanayi.

Masu shirya zanga-zangar dai sun ce akalla mutane dubu 40 ne suka yi gangamin yayinda jami’an ‘yan sandan kasar ta Faransa suka yi ikirarin cewa mutane dubu 29 ne kadai suka amsa kiran zanga-zangar a yau Juma’a.

A cewar mashiryin zanga-zangar mai taken matasa ga kalubalen dumamar yanayi, Greta Thunberg dan Sweden mai shekaru 16, zanga-zangar gudana a birane dubu biyu na kasashe 123, inda kuma ake saran ci gabanta gobe Asabar a wasu kasashe ciki har da Faransa.

A Faransar dai galibin daliban Firamare, Sakandire da kuma na Kwaleji, sun hakura da shiga ajujuwa inda suka yi dandazon a sassan kasar rike da kwalye da ke dauke da rubutun Idan ba a magance dumamar yanayi ba, babu halitta kuma babu gobe.

Akalla matasan dubu 12 ne suka yi dandazo a Lyon wasu dubu 10 kuma a Nantes yayinda wasu karin 5 da 500 kuma suka taru a Montpellier.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.