Isa ga babban shafi
Amurka

Sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin Trump da 'Yan Majalisa

A karon farko, shugaban Amurka Donald Trump, yayi amfani da karfin ikonsa na shugaba mai cikakken iko, wajen soke matakin da ‘yan majalisun kasar suka dauka, na kawo karshen dokar ta bacin da ya kafa, don samar da sama da dala biliyan 5 na gina katafariyar Katanga tsakanin Amurka da Mexico.

Shugaban Amurka Donald Trump yayin soke kudurin majalisun kasar kan ginin katafariyar katanga tsakanin Amurka da Mexico.
Shugaban Amurka Donald Trump yayin soke kudurin majalisun kasar kan ginin katafariyar katanga tsakanin Amurka da Mexico. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

A makon da ya gabata ‘yan majalisun na Amurka suka kada kuri’ar amincewa da kudurin dakatar da shirin na Trump na samar da biliyoyin dalolin, wadanda a baya aka tsara yin amfani da su wajen wasu ayyuka, ba tare da amincewar ‘yan majalisun ba.

Ministan Shari’ar Amurka, William Barr yace matakin na shugaba Trump bai saba ka’ida, sai dai kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ce a ranar 26 ga watannan zasu kada kuri’ar soke matakin amfani da cikakken ikon da Trump ya dauka.

Takaddama tsakanin shugaban Amurka da ‘yan majalisun kasar, ya jawo gurguncewar ayyukan wasu muhimman ma’aikatun gwamnati na wucin gadi a karshen shekarar bara, wanda ya zama mafi tsawo da aka taba gani a tarihin kasar.

Gurguncewar ma’aikatun gwamnatin na Amurka ya da ya shafi sama da ma’aikata dubu 800 a matakin tarayya, wadanda samun albashinsu ya tsaya cik.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.