Isa ga babban shafi
New Zealand

Rashin isasshen lokaci ne ya hana dakile harin New Zealand

Fira Ministar New Zealand Jacinda Arden, ta ce Brenton Harrison, dan ta’addan da ya hallaka masallata 50 a birnin Christchurch, ya aika mata sakon email kan shirinsa na kai harin ta’addancin, mintuna tara kafin aiwatar da shi.

Fira Ministar kasar New Zealand Jacinda Arden, yayin ganawa da iyalan Masallatan da dan ta'adda ya hallaka.
Fira Ministar kasar New Zealand Jacinda Arden, yayin ganawa da iyalan Masallatan da dan ta'adda ya hallaka. AP
Talla

Sai dai rashin isasshen lokaci ya sa jami’an tsaro gazawa wajen dakile ta’asar da ya tafka, la’akari da cewa cikin sakon da ya aike musu, bai bayyana wurin da zai kai harin ba da kuma lokacin aiwatar da shi.

Hakan a cewar Fira Ministan ta New Zealand ya haifar da aukuwar ta’addanci mafi muni da kasar ta taba gani, tuni kuma aka kara tsaurara matakan tsaro a ilahirin kasar.

Yawan wadanda dan ta’addan ya hallaka ya karu zuwa 50 ne daga 49, bayan gano Karin mutum guda a masallacin Juma’a na Al Noor, inda Brenton Harrison ya hallaka akalla mutane 40, kafin tafiya zuwa Masallacin Juma’a na gaba.

A halin da ake ciki, mutane 34 aka kwantar a asibiti bayan jikkatar da suka yi, 12 daga cikinsu kuma cikin mummunan yanayi.

A ranar Asabar aka gurfanar da Brenton Harrison mai shekaru 28 a gaban Kotu, wadda ta bada umarnin ci gaba da tsare shi, har zuwa 5 ga watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.