Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta karfafa tsaro sakamakon tarzomar ranar Asabar

Fraministan Faransa Edourd Philippe, ya sanar da sabbin matakan tsaron da gwamnatin kasar za ta fara dauka bayan zanga-zangar masu riguna dorawa a ranar Asabar da ta juye zuwa tarzomar a birnin Paris, matakin da ya kai ga kone shaguna da dama, tare da sace dukiya mai tarin yawa.Cikin matakan a cewar Firaministan sun hada da haramta gudanar da zanga-zanga a wasu sassa na kasar musamman birnin Paris baya ga daukar matakin sauya kwamishinan ‘yan sandan birnin na Paris. 

Zanga-Zangar ta ranar Asabar dai ta haddasa asarar tarin dunkiya a sassan kasar ta Faransa
Zanga-Zangar ta ranar Asabar dai ta haddasa asarar tarin dunkiya a sassan kasar ta Faransa REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Yayin zanga-zangar ta ranar Asabar da ta juye zuwa tarzoma dai an yi ta aragama tsakanin jami'an tsaron kasar ta Faransa da gungun masu riguna dorawa, matakin da gwamnatin kasar ta amsa cewar tabbas matakan tsaronta sun gaza, wajen dakile tarzomar.

Zanga-zangar wadda ta adawa ce da gwamnatin Shugaban Macron  ita ce karo na 18, da masu rigunan dorawar ke gudanarwa kowane karshen mako, sai dai a wannan karon zanga-zangar ta juye zuwa tarzoma.

Cikin jawaban Firaminista Edouard Phillippe, ya ce bisa abubuwan da suka faru tabbas lamarin ya nuna cewa hukumomin tsaron kasar sun tafka wasu kura-kurai wadanda ya sanya tilas gwamnati ta gaggauta gyarawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.