Isa ga babban shafi

New Zealand ta karfafa tsaro a makarantu, asibitoci da wuraren ibada

Gwamnatin New Zealand tace za ta karfafa matakan tsaro a makarantu da asibitoci da kuma wuraren ibada daga yau Litinin, sakamakon kazamin harin da aka kai Masallatan Juma’a wadanda suka yi sanadiyar hallaka mutane 50.

Wasu jami'an tsaron New Zealand yayin baiwa wuraren Ibada musamman Masallatai tsaro.
Wasu jami'an tsaron New Zealand yayin baiwa wuraren Ibada musamman Masallatai tsaro. AP/Mark Lennihan
Talla

Fira Ministar kasar Jacinda Ardern ta bayyana haka bayan ta ziyarci al’ummar Musulmin Wellington inda ta bayyana alhinin mutanen kasar kan harin.

Yayin jawabi a Wallinton, Fira Minista Jacinda Arden tace ofishin ta da wasu jami’an gwamnati 30 sun samu wasu takardun bayanai akalla mitina 9 kafin kai harin ta'addancin.

Arden tace bayanan basu kunshi inda za’a akai harin da kuma cikaken bayani ba, sai dai cikin mintina biyu da samun bayanan an mikawa jami’an tsaro domin daukar mataki.

Tuni dai aka gurfanar da dan ta'addan da ya bude wuta kan Masu Ibada a Masallatan Juma’an guda biyu a gaban kotu.

An gurfanar da dan ta'addan Brenton Harrison, dan kasar Australia mai shekaru 28, a gaban babbar kotu da ke birnin na Christchurch a yau Asabar, wadda ta bada umarnin a ci gaba da tsare shi, zuwa 5 ga watan Afrilu, lokacin zamanta na biyu a kan ta’addancin da yayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.