Isa ga babban shafi
Tarayyar-Turai

EU za ta daina sayen jiragen yaki marasa matuka daga Amurka

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta sanar da ware sama da yuro miliyan 500 a kasafinta ga bangaren tsaro da kuma bunkasa samar da jirage marasa matuka ga nahiyar.

Nau'ikan jirage marasa matuka samfurin Amurka
Nau'ikan jirage marasa matuka samfurin Amurka Vincenzo PINTO / AFP
Talla

Cikin sanarwar da kungiyar ta EU ta fitar a Brussels, ta ce cikin kasafin bangaren tsaron na fiye da yuro miliyan dari 5, kimanin yuro miliyan 100 kai tsaye zai tafi bangaren bunkasa shirin samar da jirage marasa matuka samfurin nahiyar, a wani mataki na rage dogaro ga Amurka.

A cewar kwamishinan da ke kula da harkokin kudi na kungiyar EU Jyarki Kataine, yunkurin wani mataki ne na rage kudaden da EU ke bannatarwa a bangaren sayo kayakain tsaro daga Amurka, baya ga karfafa shirye-shiryensu na cikin gida.

Kataine ya ce tsaro shi kadai ne hanyar da ayanzu na nahiyar Turai ke bukatar a mayar da hankali don bai wa al’ummarsu kariya, dai dai lokacin da zaman lafiyar duniya ke kara sukurkucewa.

Ka zalika EU ta ce nan gaba kadan za ta gabatar da wasu sabbin ayyukan ci gaban kasashenta da za su kunshi muhimman bangarori biyar ciki har da bangaren fikira da zai lashe fiye da yuro miliyan 180 ka na tsaron bangarorin sadarwa da kuma bayar da kariya ga yanar gizo don kaucewa hare-hare wanda shima ya ke bukatar yuro miliyan 7 da rabi, duk dai a yunkurin samar da cikakken tsaro ga al’ummar nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.