rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

New Zealand Hakkin Dan Adam Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

New Zealand ta zurfafa bincike kan kisan gillar da aka yiwa Musulmi

media
Fira Ministar kasar New Zealand Jacinda Arden. REUTERS/Edgar Su

Fira Ministar New Zealand Jacinda Ardern ta bada umurnin gudanar da bincike mai zaman kan sa kan kisan gillar da aka yiwa Musulmin kasar a Masallacin Juma’a, domin gano ko hukumomin tsaron kasar na iya dakile harin kafin aukuwarsa.


Ardern, ta bayyana cewar an kafa hukumar binciken shari’a domin gano yadda dan bindiga guda ya kasha mutane 50 a harin da ya girgiza duniya.

Firaministar tace yana da matukar muhimmanci a gano yadda aka aiwatar da wannan harin ta’addancin da kuma ko ana iya hana aukuwar sa.

Ardern ta bayyana cewar basa tunanin sake dawo da hukuncin kisa akan dan ta’addan Brenton Tarrant da ake zargi da aikata kisan.