Isa ga babban shafi
Brexit

Majalisar Birtaniya ta yi watsi shawarwari 8 kan Brexit

Majalisar dokokin Birtaniya ta yi watsi da wasu shawarwari guda 8 da aka gabatar jiya Laraba kan yadda kasar za ta janye daga cikin kungiyar kasashen Turai.

Kakakin majalisar dokokin Birtaniya John Bercow.
Kakakin majalisar dokokin Birtaniya John Bercow. UK Parliament/Mark Duffy/REUTERS
Talla

Daga cikin shawarwarin da aka yi watsi da su, harda wadanda ‘yan majalisar ne suka bayar da su.

Wadannan shawarwari sun hada da yiwuwar janyewa ba tare da an cimma jituwa ba, da samar da sabon tsarin karbar haraji tsakanin kasar da kuma yankin Turai, ko kuma kasar ta jingine batun janyewar daga Turai baki daya.

Kafin kada wannan kuri’a, sai da Fira Minista Theresa May ta yi alkawarin cewa za ta yi marabus daga mukaminta kafin zagaye na gaba na tattaunawar da za a yi tsakanin Birtaniya da kungiyar ta Turai.

Sanarwar ta May, ita ce ta baya bayan nan a dambarwar barin Tarayyar Turai da aka shafe shekaru uku ana yi.

Tun da farko ranar 29 ga watan Maris aka tsara Birtaniya za ta fice daga Tarayyar Turai, amma a makon da ya gabata, Tarayyar ta kara mata wa’adin zuwa ranar 12 ga watan Afrilu mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.