Isa ga babban shafi
New Zealand

An gudanar da taron tunawa da Musulman New Zealand

An gudanar da gagarumin taron tunawa da Musulmai 50 da aka kashe a Masallantan birnin Christchurch na New Zealand, taron da ya samu halartar wakilan kasashen duniya kusan 60.

Al'ummar New Zealand sun bayyana damuwa kan harin Masallatan birnin Christchurch
Al'ummar New Zealand sun bayyana damuwa kan harin Masallatan birnin Christchurch REUTERS/Edgar Su
Talla

Wani Mutun da ya tsira da ransa a kazamin farmakin, Farid Ahmed ya shaida wa dubban jama’ar da suka halarci taron cewa, ya yi afuwa ga dan bindigar da ya kashe masa mata a Masallacin na Christchurch.

Ahmed da aka turo shi a keken guragu ya ce, ya zabi zaman lafiya kuma ya yafewa maharin mai rajin fifita farar fata. Kana ya bukaci daukacin al’ummar New Zealand mabiya addinai daban daban da su yi watsi da kiyayyaya.

Firaministar kasar, Jacinda Ardern sanye da tufar gargajiya na cikin dimbin jama’ar da suka tashi tsaye tare da sunkuyar da kai a daidai lokacin da ake karanta sunayen Musulman da aka kashe a harin.

Firaministar mai shekaru 38 da ta sha yabo daga sassan duniya, ta jinjina wa ‘yan kasar kan yadda suka rungumi jama’ ar Musulmai tun bayan aukuwar kazamin harin.

Ardern ta jaddada cewa, tabbas akwai matsalar wariyar launin fata, amma ba za su yi marhabin da ita ba a kasarsu.

A bangare guda, mawakin Birtaniya Cat Stevens da ya musulunta tare da sauya sunansa zuwa Yusuf Islam, ya gabatar da wakarsa mai taken "Peace Train" a taron na tunawa da mamatan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.