rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Slovakia Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zuzana Caputova ta lashe zaben kasar Slovakia

media
Zuzana Caputova matar da ta lashe zaben kasar Slovakia REUTERS/David W Cerny

A fafatawa da ta hada yan takara biyu a zaben Shugabancin kasar Slovakia, karo na farko a tarihin kasar Uwargida Zuzana Caputova mai shekaru 45 ta lashe zaben .

An dai haife ta ranar 21 ga watan yuni na shekara ta 1973.


Uwargida Zuzana ta yi takara da Maros Sefcovic mai shekaru 52 wanda duk da goyan baya da ya samu daga bangaren gwamnatin kasar ya kasa samun rijaye a zaben.

Wannan dai ne karo na farko da aka samu mace da ta shugabanci kasar Slovakia.

Yan kasar da dama ne suka bukaci ganin an samu sauyi dange da shugabancin wannan kasa.