rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Tattalin Arziki Birtaniya Faransa Jamus

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Binciken Panama ya taimaka wajen kwato sama da dala biliyan 1 na haraji

media
Les enquêteurs allemands ont pour leur part rapatrié Daga watan Agusta na 2016 zuwa yanzu, an gudanar da bincike kan laifukan gujewa biyan haraji har kashi 500. KACPER PEMPEL/REUTERS

Shekaru uku bayan bankado badakalar Panama Papers", ta kaucewa biyan haraji, kasashe 22 da ke fama da matsalar sun yi nasarar kwato kimanin dalar Amruka bilyan 1 da miliyan 200 da aka karkatar.


Kasa ta farko daga cikin jerin kasashen da ta kwato adadi mafi yawa na kudaden da aka karkatar don gujewa harajin ita ce, Britaniya wadda ta yi nasarar karbo dala miliyan 252.

Jamus ke biye da ita, wadda ta kwato dala miliyan 183 sai kuma ta ukunsu Faransa da ta karbo adadin dalar Amruka miliyan 136, da aka karkatar.

Jaridar Le Monde ta bayyana cewa, a Faransa inda yanzu haka aka rufe binciken, kasar ta karbi kimanin euro miliyan 120, da suka hada da kudaden tara da kuma na gyaran hali.

Daga watan Agusta na 2016 zuwa yanzu, an gudanar da bincike kan laifukan gujewa biyan haraji har kashi 500, wanda ya bada damar gano badakalar karkatar da kudaden guda 415.