Isa ga babban shafi
Birtaniya-Turai

EU na duba yiwuwar karawa Birtaniya wa'adin ficewa

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai na shirin karawa Firaministar Birtaniya Theresa May wa’adin ficewa daga EU bayan bukatar hakan da ta gabatar gaban Emmanuel Macron na Faransa da Angela Merkel ta Jamus a jiya Talata.

Shugaba Emmanuel Macron yayin ziyarar da Firaministar Birtaniya Theresa May, ta kai fadarsa a jiya Talata
Shugaba Emmanuel Macron yayin ziyarar da Firaministar Birtaniya Theresa May, ta kai fadarsa a jiya Talata REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Wannan dai ne karo na biyu da Theresa ke neman karin wa’adin ficewar daga EU, dai dai lokacin da take ci gaba da tattaunawa da Jam’iyyar Labour can a gida Birtaniya don ganin kasar ta kaucewa fita daga gungun kasashen na Turai ba tare da yarjejeniya ba.

Gabanin zuwanta birnin Paris na Faransa a yammacin jiya Talata, Theresa May tun farko sai da ta fara ziyartar takwararta ta Jamus Angela Merkel don ganin itama ta mara mata baya yayin taron kungiyar ta EU da zai gudana a yau Laraba.

Shugaba Emmanuel Macron wanda ke matsayin jigo kuma mai fada aji cikin majalisar kolin kungiyar ta EU, ya ce za su iya amincewa kara wa’adin amma kar ya dara ko gaza shekara guda, yayinda itama Angela Merkel ke ganin kamata ya yi Birtaniya ta yi hakuri da batun ficewar zuwa farkon shekarar 2020 don kammala fita cikin nutsuwa.

Ilahirin shugabannin biyu da May ta ziyarta a jiya sun nuna rashin jin dadinsu da yadda Birtaniyar ke kokarin ficewa ba tare da cimma yarjejeniya ba.

Gwamnatin Faransa dai na ra’ayin cewa kamata ya yi Birtaniyar ta janye hannu daga wasu al’amuran kungiyar ta EU matukar aka kara mata wa’adin wadanda suka kunshi batub kasafin kudin shekaru 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.