Isa ga babban shafi
Turai

Zanga-zanga a Faransa a lokacin da ake dakon sanarwar Shugaban kasar

Dubban masu zanga-zanga da Gwamnatin Faransa sun sake fitowa zanga zanga a karo na 22, don sake nuna bijirewar su da manufofin shugaba Emmanuel Macron, a daidai lokacin da ake jiran Shugaban kasar Emmanuel Macron ya aiwatar da sauye-sauye da Gwamnatin Faransa zata gabatarwa yan kasar.

Taron masu zanga-zanga a Paris na kasar Faransa
Taron masu zanga-zanga a Paris na kasar Faransa Sebastien RIEUSSEC / AFP
Talla

A makon da ya gabata dai ne gwamnatin Faransa ta soma duba wasu daga cikin bukatun yan kasar ,bayan da aka share yan kwanuki ana tafka muhara dangane da batutuwan da suka jibanci tattalin arzikin kasar .

An jima yan kasar ta Faransa na kallon Gwamnatin shugaba Emmanuel Macron a matsayin dutsen nika.

A ranar litinin da ta gabata kafafen yada labaren kasar sun share lokaci suna ta nuna yan kasar a lokacin tattaunawa kai tsaye da Shugaban kasar Emmanuel Macron, inda suka nuna masa karara cewa siyasar sa ta fuskar tattalin arziki ba za ta haifar da damin ido ba.

Wasu daga cikin yan kasar sun bayyana ta yada wannan gwamnati ke kokarin talautar da marasa karfi, sun kuma hango cewa masu hannu da shuni na amfana da wannan gajiya da Gwamnati take kokarin kawowa.

Ga baki daya Shugaban kasar Emmanuel Macron ya dau alkawalin sake duba rawar siyasar da gwamnatin sa zata taka nan gaba, da nufin samarwa al’uma kayakin more rayuwa cikin wadata.

Yan kasar na dakon sanarwar Shugaba Emmanuel Macron wanda ake sa ran zai kawo sauyi ga siyasar tattalin arzikin Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.