Isa ga babban shafi
Turai-Mafia

Barazanar kungiyoyin Mafiya ta fi 'yan cirani illa a Turai-'Yan sanda

Shugaban rundunar 'yan sandan Turai Jari Liukku ya bayyana cewar kungiyar masu aikata laifuffuka ne yanzu haka ke haifar da babbar barazanar tsaro a nahiyar baki daya, ganin yadda matsalar su ta zarce ta ayyukan ta’addanci da kwararan baki zuwa yankin.

Wasu Jami'an 'yansanda lokacin da su ke tsaka da rangadi
Wasu Jami'an 'yansanda lokacin da su ke tsaka da rangadi Reuters/路透社
Talla

Shugaban Yan Sandan Turan Jari Liukki ya bayyana irin wadannan kungiyoyin masu aikata laifi da ke yi wa nahiyar Turai barazana da suka hada da 'yan kungiyar mafiya da ke Italia da Albania ad Gabashin Turai da kuma kungiyar masu amfani da Babura wadanda aka haramta.

Jami’in ya ce suma 'yan kasashen Asia da Afirka da kuma Amurka ta kudu na yi wa yankin barazana, sai dai bata kai irin na wadancan kungiyoyi ba.

Liukki ya ce babu yadda za a samu nasarar dakile wadannan kungiyoyi ba tare da hadin kai da sauran kasashen duniya ba, domin ko su kungiyoyin sukan hada kai da takwarorin su da ke wasu nahiyoyi.

Daraktan yaki da kungiyar mafia a kasar Italia, Giuseppe Governale ya bayyana kungiyoyi irin su Sicilian Cosa Nostar da Calabrian Ndrangheta da Neapolitan Camorra a matsayin manyan kungiyoyin mafiyar duniya.

Governale ya ce dakile halarta kudaden haramun na daya daga cikin matakan murkushe wadannan kungiyoyi da suka dogara da samun kudade wajen gudanar da ayyukan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.