Isa ga babban shafi
Ukraine

Shugaba Poroshenko ya amsa kaye a zaben Ukraine

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya amince da shan kaye a zaben kasar da ya gudana yau Lahadi, inda ya taya takwaransa Volodymyz Zelensky murnar nasarar lashe zaben.

Shugaba Petro Poroshenko mai barin gado tare Volodymyr Zelenskiy shugaban Ukraine mai jiran gado
Shugaba Petro Poroshenko mai barin gado tare Volodymyr Zelenskiy shugaban Ukraine mai jiran gado REUTERS/Valentyn Ogirenko
Talla

Shugaba Poroshenko wanda ya kira Zelensky na jam’iyyar adawa kuma fitaccen dan wasan barkwancin da suka yi takara tare, ya kuma taya shi murnar nasarar lashe zaben, ya ce zai ci gaba da fafatawa a fagen siyasar kasar.

A cewar shugaban mai baring ado, bangaren adawa ya samu rinjayen akalla kashi 73 wanda ke nuna cewa ya sha kaye, sai dai rashin nasarar ta sa bata nufin zai bar harkar siyasa.

Cikin jawaban shugaban mai barin gado, ya ce ya gamsu da dukkanin matakan da hukumar zaben kasar ta bi wajen ganin ta gudanar da sahihin zabe, kuma a shirye ya ke ya fice daga Ofishinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.