Isa ga babban shafi
EU

Shugabannin EU na sasanta Serbia da Kosovo

Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai da ke gudanar da wani taro a birnin Berlin a wannan Litinin, na shirin maido da kasashen Serbia da Kosovo da basa ga maciji da juna kan teburin tattaunawar zaman lafiya.

Kasashen Turai na ci gaba da kokarin dinke barakar da ke tsakanin Kosovo da Serbia da ke yankin Balkans
Kasashen Turai na ci gaba da kokarin dinke barakar da ke tsakanin Kosovo da Serbia da ke yankin Balkans Manuel ELIAS / UNITED NATIONS / AFP
Talla

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ke karbar bakwancin Serbia da Kosovo masu hamayya da juna, wadanda kuma alakasru ta dada tsami a cikin ‘yan watannin nan, yayinda a gefe guda, akwai sauran shugabannin kasasshen yammacin yankin Balkans da mambobin kungiyar tarayyar turai da Croatia da Slovenia da ke halartar taron na Berlin a wannan Litinin.

Taron ya mayar da hankalinsa ne kan batun zaman lafiya a yankin Balkans, tare da muhimmanta hanyar farfado da tattaunawa tsakanin Kosovo da Serbia kamar yadda fadar shugaban Faransa ta bayyana a cikin wata sanarwa gabanin bude zaman na yau.

Taron wanda Merkel da Macron suka shirya na zuwa ne bayan tattaunawar da Kungiyar Tarayyar Turai ta jagoranta tsakanin Serbia da Kosovo ta tabarbare a shekarar bara.

Tattaunawar da EU ta jagoranta a barar, ta tabarbare ne saboda batun sauye-sauye akan iyakokin kasashen biyu masu makwabtaka da juna, abinda ya haifar da caccakar juna a tsakaninsu.

Tankiyar da ke tsakanin kasashen biyu ta samo asali ne bayan Serbia ta haramta wa Kosovo ‘yancin kanta, wadda a can baya ta kasance lardi mai dimbin tarihi da al’adu ga Sabiyawan da suka balle bayan yakin 1998-1999.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.