Isa ga babban shafi
Spain-Venezuela

Spain ta gargadi Guaido kan yunkurin juyin mulki a Venezuela

Gwamnatin Spain ta yi gargadi kan yiwuwar fuskantar zubar da jini a Venezuela, dai dai lokacin da jagoran adawa Juan Guaido ke ikirarin samun goyon bayan sojin kasar.

Firaministan Spain Pedro Sanchez
Firaministan Spain Pedro Sanchez 路透社。
Talla

A jawaban kakakin gwamnatin Spain ga manema labarai, Isabel Celaa ya ce Spain na fatan ganin an kawo karshen rikicin Venezuela cikin salama ba tare da an zubda jini ba.

Haka zalika Spain goyon bayan kasar dari bisa dari wajen ganin an gudanar da sahihin zabe don mika gwamnati salin’alin ba tare da kifar kifar da gwamnati mai ci ta hanyar juyin mulki ba.

Kalaman gwamnatin Spain din na zuwa ne bayan wani taron manema labarai da Juan Guaido ya kira da ya ke shaidawa manema labarai cewa yanzu ya na da cikakken goyon bayan sojin kasar, kuma zai iya karbar mulki cikin sauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.