Isa ga babban shafi
Tarayyar turai

EU ta fitar da tsarin tafiyar da kungiyar bayan Brexit

Shugabannin kasashen Turai EU, sun bayyana jerin tsare-tsaren da za su yi amfani da su wajen gudanar da kungiyar da karfafa tattalin arzikinta bayan kammala ficewar Birtaniya daga cikinsu. A yayin taron da ya gudana a birnin Sibiu da ke Romania, manbobin na EU sun amince cewar, ficewar Birtaniya daga cikinsu ba za ta haifar da yunkurin wasu kasashen na bin sawunta ba.

Shugabannin Kasashen Turai a taronsu na birnin Sibiu
Shugabannin Kasashen Turai a taronsu na birnin Sibiu Ludovic Marin/Pool via REUTERS
Talla

Birtaniya da har yanzu bata kammala cika sharuddan rabuwa da EU ba, ita kadai ce bata halarci taron na birnin Sibiu ba.

Taron ya amince da muhimman kudurori guda 10 da kasashen Turan suka yi alkawarin mutunta su.

Muhimmai daga cikinsu kuma sun kunshi hada kai a duk lokacin da suka tunkari magance kalubalen da ya bijiro musu, tabbatar da daidaton adalci da kuma tsara manufofin da za su amfani al’ummar nahiyar Turan da ke tafe nan da shekaru masu yawa.

Sauran kudurorin da kasashen na EU suka cimma a taron sun hada da bai wa junansu damar cimma burin da suka sanya a gaba, kare tsarin tafiyar da rayuwarsu, dimokaradiya da kuma bin doka da oda, sai kuma tabbatar da kungiyar EU a matsayin jagora mai kima a idon duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.