Isa ga babban shafi
Turai

Julian Asange zai sake komawa Kotu

Masu gabatar da kara a Sweden sun bayyana sake bude bincike kan zargin aikata fyade da ake yiwa Julian Assange, mai shafin Wikileaks na fallasa bayanan sirri, laifin da ake zargin ya aikata shi a shekarar 2010.

Julian Assange, jagoran shafin  Wikileaks yan lokuta bayan cafke a ofishin jakadancin Ecuado
Julian Assange, jagoran shafin Wikileaks yan lokuta bayan cafke a ofishin jakadancin Ecuado REUTERS/Henry Nicholls
Talla

Lauyoyin a karkashin Jagorancin mataimakiyar masu gabatar da karar a kasar ta Sweden, Eva-Marie Persson, na dai fatan ganin an hukunta Assange kafin karewar wa’adin dokar da ke shafe laifi daga kan wanda ake zargi bayan kaiwa adadin wasu shekaru, akalla10, ba tare da daukar mataki akansa ba.

Sai dai a nashi bangaren Julian Assange ya bayyana sabunta bincike kan zargin da ake masa da cewa hanya ce kawai ta neman mika shi ga Amurka, inda yake fargabar fuskantar hukunci, saboda fallasa wasu bayanan sirrin gwamnatin kasar da yayi a shekarun baya.

Cikin watan Mayu na 2017, aka dakatar da binciken na zargin Assange da aikata Fyade, wanda acewar masu gabatar da karar sun yi haka ne ba don rashin hujjoji ba, sai don fuskantar kalubalen da ke yiwa aikin gudanar da binciken barazana.

Mai shafin na wikileaks da ke fallasa bayanan na sirri dai ya shafe shekaru 7 yana gudun hijira a Ofishin Jakandancin Ecuador da ke Birtaniya, donn kaucewa maida shi zuwa Sweden, a ranar 11 ga watan Afrilu kuma aka kama shi da taimakon kasar Wcuador, daga bisani wata koto a London ta yanke masa hukuncin daurin makwanni 50, saboda saba ka’idoji ko Umarnin gwamnatin Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.