Isa ga babban shafi
Faransa

Masu zaman kashe wando sun ragu a Faransa

A karon farko cikin shekaru 10, an samu raguwar marasa aikin yi a Faransa, kamar yadda alkaluman da hukumomin kasar suka fitar a wannan Alhamis ke nunawa. Wannan na zuwa ne a yayinda gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ke fafutukar sauya dokokin ma’aikata a kasar.

Hukumar Kididdiga ta Faransa, INSEE ta ce an samu raguwar masu zaman kashe wando a karon farko cikin shekaru a kasar
Hukumar Kididdiga ta Faransa, INSEE ta ce an samu raguwar masu zaman kashe wando a karon farko cikin shekaru a kasar LOIC VENANCE / AFP
Talla

Hukumar Kididdigar kasar ta INSEE ta ce, rashin aikin yi ya ragu zuwa kashi 8.7 daga kashi 8.8 a cikin rubu’in farko na wannan shekarar, kuma a karon farko kenan da ake ganin haka tun shekarar 2009.

Wannan ci gaban da aka samu zai rage matsin lambar da shugaba Emmanuel Macron ke fuskanta musamman daga bangaren masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da wasu sauye-sauyen gwamnati.

A shekarar farko ta mulkinsa a 2017, shugaba Macron ya bukaci bullo da tsarin magance matsalar zaman-kashe wando ta hanyar sauya dokokin ma’aikata domin bayar da damar dauka da sallamar ma’aikaci cikin sauki, abinda da kamfanonin kasar suka jima suka dako.

Bayanai na cewa, tattalin arzikn Faransa ya shafe tsawon shekaru uku a jare yana habbaka ba tare da samun koma-baya ba, abinda ya sa tattalin arzikn kasar ya sha gaban na Jamus da Italiya wajen bunkasa.

Kodayake har yanzu, alkaluman rashin aikin yi ya ninka sauya biyu a Faransa idan aka kwatanta da kasar Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.